A ‘yan makonnin da suka gabata an sami rahotan sace sacen mutane a yankin kananan hukumomin Tudunwada da Kibiya da Rano da Sumaila da Takai da kuma Doguwa dake yankin kudancin Kano.
Dangane da wannan kalubale rundunar ‘yan sandan ta Kano ta ce ta saka kaimi wajen farautar wadanda ake zargi da aikata wannan laifi.
DSP Magaji Musa dake zaman kakakin rundunar yace sun kama mutanen da ake zargi bayan sumame da jami’an su kai maboyar bata garin dake cikin dajin Falgore dake tsakanin kaniyakar jihar Kano da Plato da kuma jihar Bauchi.
Yace bayan nasarar kama tsagerun su 32, ‘yan sanda su sami bundigogi da albarusai da katinan wayar salula da kudi da sauran ababe da batagarin ke amfani dasu
Wasu daga cikin wadanda suka tsallake rijiya da baya daga kamen masu garkuwa da mutane zuwa dajin na Falgore sunce sun kubuta daga hannun tsagerun bayan sun tafi da su cikin daji.
Haka zalika, wani dattijo da tsagerun suka kama ‘dan sa suka tafi dashi cikin dajin na Falgore ya fadawa manema labarai cewa, daga bisani sun saki dan nasa a cikin daji kuma ya dawo gida.
Hon Zubairu Hamza Massu dan amajalisar dokokin jihar Kano ne mai wakiltar mazabar Sumaila , ya biya kudin fansa ga tsagerun bayan da suka sace mahaifinsa a kauyensu na Massu a cikin watan jiya, baya ga godiya ga Allah, ya yaba da kokarin ‘yan sandan na kakkabe bata gari daga yankin baki daya.
Saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari daga Kano.