Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bada umarnin cewa daga yanzu kada Fulani makiyaya, su bar Shanun su su shiga karkara suna kiyo sai dai su bar su waje daya suna basu ciyawa.
Alhaji Muhammadu Nasamu, shugaban kungiyar Miyetti Allah rashen jihar Ekiti, yace suma ‘yan jihar Ekiti, ne yana mai cewa suna kira ga Gwamnatin tarayyar Najeriya,da ta tsoma baki a wannan lamari.
Yakara da cewa wannan yana iya jawo rashin jituwa ta yadda matasan gari zasu iya cutar dasu da dukiyoyin su, yana mai cewa yanzu Fulanin jihar Ekiti suna cikin matsala.
Wani lauya Surajo Danbaba, yace abinda Gwamna ke dogaro dashi shine sashe na 45, na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda tace akwai lokacin da Gwamna zai iya hanna zirga zirga idan na ganin cewa akwai matsala.