Hedkwatar tsaron Najeriya tace rundunar hadin guiwa ta cafke kwamandojin mayakan Boko Haram biyar a kasr Kamaru, bayan da suka tsere daga dajin Sambisa.
Hedkwatar tsaron Najeriyar, tace sun wadannan kwamandojin Boko Haram, biyar da aka cafke a kasar Kamaru an fafaresu ne daga dajin Sambisa, inda suka nausa arewacin Kamaru, suka kumyi sansani a dajin Madawaya, inda mayakan hadin guiwa na kasashen yakin Tafkin Chadi, suka cafke su.
Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya, janar Rabe Abubakar, yace bayanai na siri irin na Soja ne ya bada damar damke wadannan mayaka, ya kuma kara da cewa duk abinda za suyi domin magance matsalolin ta’addanci za suyi.
Kwararre a sha’anin tsaron Dr. Bawa Abdullahi Wase, yace duk wadanda keda zummar tada kayar baya sukan nemi mafaka ne tsakanin gari da gari ko jihar da jihar ko kuma kasa da kasa.
Kakakin rundunar kasashen yankin tafkin Chadi, dake yaki da Boko Haram Kanal Muhammad Dole, yace a cikin tsarin da aka yi an raba Sojoji a muhimman wurare a kasashen masu makwabtaka da tafkin Chadi.