Muhawarar ta karshe kuma ta ukku an yita ne tsakanin Hillary Clinton ta jam'iyyar Democrat da Donald Trump na jam'iyyar Republican, kuma ta shiga tarihi a matsayin wadda aka fi kalla a duk fadin duniya.
Muhawarar ta ja hankalin mutanen kasashe masu tasowa kamar Najeriya abun da ya sa wasu suka yi tsokaci kan abubuwan da suka ji.
A muhawarar Donald Trump yana korafin wai ana son a yi masa magudi ko kuma an riga an yi saboda haka ya ki fadin zai amince da sakamakon zaben ko ba zai yi ba wai sai yayi binciken kwakwaf.
'Yan takarar sun shafe awa guda da rabi suna caccakar juna.
A Yola fadar jihar Adamawa wasu sun tofa albarkacin bakinsu. Muhammad Usman Tukur yace muhawarar ta ta'allaka ne akan abubuwaa ukku. Hillary Clinton ta zargi abokin hamayyarta da rashin biyan haraji. Yakamata a ce duk wanda yake neman ya shugabanci jama'a to ya zama misali na kwarai, mai bin doka da biyan haraji. Ya lura kuma da rashin da'ar Trump wanda ya dinga tsoma baki duk lokacin da Clinton take magana.
Aliyu Umar yace yana ganin makama ta karewa Trump domin babu abun da yake fada sai zargi. Haka ma yake korafin ba'a yi masa adalci ba kuma hatta zaben yace an riga an yi magudi. Yana ganin Clinton tayi rinjaye.
Malam Yakubu Isa yace akwai daratsi da kasashe masu tasowa ya kamata su koya. A kasashen Afirka ne ake anfani da banbancin jinsi ko kabila ko addini idan an zo zabe amma a kasashe kamar Amurka babu ruwansu da wadannanan illa dai ka gaya masu abun da zaka yi. Amma Trump ya fara da cewa zai kori bakin haure tare da musulmai da barazanar gina shingen takanga tsakanin Amurka da Mexico.
Ga rahoton Abdulaziz Ibrahim da karin bayani.