MDD na fatan wannan tsagaita wutar zai bada ma’aikatar agaji daman shiga da kayan agajin ga masu tsananin bukata kazalika zai kuma bude hanayar tattaunawar zaman lafiya.
Wannan tsagaita wuta ta sa’o’I 72 ne amma tana yuwa ayi wani Karin lokaci kan kwanaki ukun farkon.
Wannan shirin ya biyo bayan bazuwar soji a arewacin Yeman, inda Saudi Arabiya ke goyon bayan rundunar mayakan yan tawaye wanda ke gaggauta dannawansu zuwa garin Saada wanda shine babban mazaunin mayakan Houti.
Yakin na Yemen ya barke ne a cikin shekarar 2014 a lokacin da yan tawayen Shi’a da aka fi sani da Houti dake zaune a Arewacin kasar suka kwace babban birnin Sana’a daga bisani suka zarce zuwa sauran yankunan kasar masu rauni.
A cikin watan Maris 2015, Saudi Arabiya da kawayenta na kasashen yankin Gulf suka kaddamar da hare hare da ta sama a kan yan tawayen. Wannan dai shine karo na shida da ake kokarin kawo karshen zub da jinin.
MDD na kimanta akalla fararen hula dubu hudu ne aka kashe tun fara yakin a watan Maris 2015, kuma galibinsu duk sun mutu ne a sanadin haren-jiragen saman da ake kaiwa a karkashin jagorancin Saudi Arabiya.