Wata kungiyar ‘yan bindiga dauke da manyan makamai gami da ‘yan kunar bakin wake sun afkawa ginin kafar yada labarai ta kasa dake gabashin Afghanistan, inda suka kashe kusan mutane biyu da kuma raunata kusan wasu 20, a cewar Jami’ai.
Jami’ai sun ce nan take jami'an tsaron Afghanistan suka kewaye ma’aikatar inda suka kashe maharan a fafatawar da suka yi don kawo karshen kawanyar da suka yiwa wurin.
Jami’ai da kuma wadanda abin ya faru akan idonsu sun fadawa manema labaran yankin cewa harin na yau Laraba da aka yi a Jalalabad, babban birnin yankin Nangarhar, ya fara ne a lokacin da ‘yan kunar bakin wake suka tarwatse kawunansu domin ba sauran maharan damar kutsawa cikin ginin gidan radiyo da talabijin na kasar Afghanistan da akae kira RTA a takaice.
Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin.
Facebook Forum