Babban hafsan, wanda shine mukaddashin kwamanda rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci mai kula da tara bayanan sirri da aikace aikace a fafatawar da suke yi da ISIS, wanda yake Iraqi, ya gayawa manema labarai ta bidiyo daga Bagadaza cewa, tsakanin mayakan sakai 1,500-zuwa 2000 ne suke shiga kasashen biyu ko wane wata a dai dai wannan lokaci bara lokacinda ya kama aiki a can, amma yanzu kamar mutum metan ne suke zuwa yankin.
Haka nan Janar Gersten yace, sun lura da cewa mayakan sakan masu yawa suna barin kungiyar, ISIS, kuma yanzu kam ta ma kasa biyan mayakan nata albashi.
Ahalinda ake ciki kuma,masu bincike da suka hallara a babbar makabartan soja ta Arlington a jihar Virginia da bashi da nisa da nan birnin Washington, sun yi zargin cewa duk da karin kudi da kokarin da rundunar sojin Amurka tayi wajen rage yawan tarzoma da kuma ilmantar da sojoji kan illar tilasta mata kwanciya da maza, har yanzu ana ci gaba da fuskantar wannan matsala.