Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Syria ta kara wa'adin tsagaita wuta a yankin Aleppo


Shugaban Syria Bashar al-Assad.
Shugaban Syria Bashar al-Assad.

Gwamnatin Syria ta sanar da sake kara wa’adin sa’o’i 48 akan karamar ‘yarjejeniyar tsagaita wutar nan da ake ta riritawa a Aleppo, inda rikicin gwamnati da ‘yan tawaye ke barazana ga yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a fadin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Syria wato SANA, ya bada rahoton cewa, rundunar sojoji ce ta bada sanarwar cewa, an kara wa’adin yarjejeniyar ta Aleppo wacce ta fara aiki a ranar Juma’a zata kuma ta kare yau Talata.

Amurka da Rasha ne suka taimaka wajen kawo yarjejeniyar tsagaita wuta a garin, kwatankwacin wacce aka samar a garuruwan Latakia da gabashin Ghouta a watan da ya gabata.

A matayin wani bangare na tabbatar da dorewar yarjejeniyar tsagaita wuta a duk fadin kasar da aka cimma a watan Fabrairun da ya gabata. Aleppo na daya daga wuraren da aka tafka mummunan fada a ‘yan makonnin baya-bayan nan.

Wanda daga watan Afirilun bana zuwa ‘yanzu aka hallaka farar hula kusan 300, abin da ya hada da hari da sama da harin da aka kai kan asibitocin garin. Amurka tace cimma kananan tsagaita wuta na da muhimmanci akan ‘yarjejeniyar tsagaita wuta a fadin kasar.

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG