Kafofin yada labarai na kasar sun ce Ministan Yawon shakatawa da bude idanu, Derek Hanekom, Da Ministan lafiya Aaron Motsoaledi da kuma Ministan Ayyuka, Thulasi Nxesi sun yi kira ga Zuma da ya sauka daga kan mulki a lokacin wani taron jam'iyya mai mulki ta ANC da aka yi a karshen mako, taron da sai da aka kara tsawonsa har zuwa yau litinin.
Mai fashin bakin harkokin Siyasa Ranjeni Munusamy Ya rubuta a shafin Yanar gizo na jaridar Daily Maverick cewa “ Ba bu makawa Zuma na yakin ceto rayuwarsa ta siyasa."
Rigingimu sun mamaye mulkin Zuma tun lokacin da ya shiga ofis, kuma ana ta samun Karin Yan jam’iyyarsa da masu raji dake kira kan ya sauka daga mulki.
“Yayi kememe kan mulki a yayin da ya bayyana cewa mafi yawan yan jam’iyyarsa ta ANC da kawayensu basa bukatar sa a matsayin shugaban kasa" in ji Munusamy. Ya kara da cewa a yanzu an fara kidaya sauran kwanakin da suka rage ma Zuma a kan mulki.
Fitar sa baza tayi sauki kamar yadda wasu ke tsammani ba. Har yanzu shugaban yana da magoya baya a cikin wasu masu rike da manyan mukamai da masu fada aji a cikin jam’iyyar ANC. Ya tsallake Kuri’ar rashin goyon baya a wannan watan a Majalisa. Babbar Jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ce ta gabatar da kudurin , inda take zargin Zuma ya baiwa Iyalin Gupta damar zaben wasu mambobi a gwamnatinsa, wanda hakan ya nuna hatsarine shi ga zaman lafiyar kasar kasar.
Haka kuma zuma ya fuskanci zazzafan kalubale akan amfani da Dalar AMurka miliyan $20 wajen gyaran gidansa na kashin kansa a wajen gari. Daga baya ya nemi afuwa ya kuma yarda zai biya wani kaso na kudin.
Jam’iyyar ANC ta Mandela ta hau kan Mulki bayan kawo karshen mulkin nuna wariya a shekarar 1994.