Aksarin wadanda aka kashe, a cewar rahotanni ‘yan kabilar Hutu ne, kuma jami’an yankin sun dora alhakin wannan aika-aika, akan tsagerun Nande, wadanda suke samun sabani da ‘yan kabilar ta Hutu a Lardin Kivu dake arewacin kasar.
Wata jami’a a yankin, ta ce da farko sai da maharan suka kai farmaki a wani dan karamin shingen binciken dakarun kasar, kafin su dangana da wajen da suka halaka mutanen.
Rikicin kabilanci da matsalar mallake yankuna da ‘yan kasashen waje ke yi, da kuma iko da arzikin kasar, na daga cikin ababan dake haddasa rikici a gabashin Congo, lamarin dake haifar da kungiyoyin ‘yan tawaye cikin shekarun kusan 20 da suka gabata.
Hakan kuma ya kaiga asarar rayukan miliyoyin mutane.