A cikin wasikar gwamnan fada cewa idan kansilolin sun cigaba da yunkurin to zasu sabawa doka lamarin da ka iya haifar masu abun da basu yi tsamnani ba.
Yanzu dai an dake taron kansilolin har zuwa wani lokacin da ba'a kayyade ba. Dama tun lokacin da kansilolin suka bada sanarwar shirin tsige magajin garin na kusa dashi suka fara kallon lamarin tamkar wata makarkashiyar siyasa.
Alhaji Nasamu Kada kusa a jam'iyyar Amin Amin wadda a karkashinta ne Hassan Sedu ya dare kujerar magajin garin Yamai nada irin wannan ra'ayin. Alhaji Kada yace mutane ne da suka yi kwangila da, suka shiga jam'iyyarsu amma suka koma jam'iyyun PNDS mai mulki da kawarta MNSD suna son su cimma burinsu.
Amma Alhaji Asumanu Muhammadou kakakin PNDS ya nisantar da jam'iyyarsa daga wannan alamarin.
Ita dai ma'aikatar magajin garin Yamai tayi fama da yaje-yajen aiki sakamakon rashin biyan albashin ma'aikata na watanni akalla biyar abun da kansiloli suka dauka wani kwakwaran hujjar tsige Hassan Seidu.
To saidai 'ya'yan jam'iyyarsa cewa suke rashin biyan ma'akata ba laifinsu ba ne. Sun ce laifin gwamnati ne ana dai son a shafa masu kashin kaza ne kawai.
Kakakin jam'iyyar PNDS Tarayya ya kara nanatawa babu hannunsu a ayyukan magajin gari saboda haka tsuntsun da ya jawo ruwa a kansa zai kare. Yace ba gwamnati ba ce take biyan albashin ma'aikatan kananan hukumomi, kuma abun mamaki ne a ce karamar hukumar birnin Yamai ta kasa biyan ma'aikatanta. Abun da ya faru shiririta ne kawai.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.