Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu da Aka Hana Tsayawa Takara A Ghana Sun Ce Ba Za'a Yi Adalci Ba


'Yan bangan siyasa na jam'iyyar NPP a kasar Ghana
'Yan bangan siyasa na jam'iyyar NPP a kasar Ghana

Wasu manyan ‘yan siyasan kasar Ghana su ukku da aka hanawa shiga takara a zaben shugaban kasan da na ‘yan majalisun dokoki da ake shirin yi a ran 7 ga watan Disamban nan mai zuwa, sun ce da kyar in za’a yi adalci a zabe.

Edward Mahama na jam’iyyar PNC da Papa Kwesi Nduom na PPP da kuma Nana Konadu Agyeman Rawlings, matar tsohon shugaban Gahna Jerry Rawlings kuma ‘yar jam’iyyar NDP, sun bayyana ra’ayinsu ne a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da suka gabatar, inda kuma suke zargin Hukumar Zabe da cewa bata yi shirin da zai sa a a sami zabe mai inganci ba.

Bayan zargin da suka yi na cewa har ila yau an hana wasu ‘ya’yan jam’iyunsu tsayawa takara ko a zaben majalisun dokoki, shugabannin jam’iyyun ukku sun ce Hukumar Zaben na shirin gudanarda zaben ba a bisa ka’idojin da aka yarda da su ba.

Sai dai kuma wani jami’in Hukumar zaben, Eric Dzakpasu, a hirar da yayi da gidan rediyon nan na Muryar Amurka, ya musanta zarge-zargen na shugabanninin PNC, PPP da kuma NDP, ya kuma ce Hukumar ba zata bari a juyarda alkiblarta na tabattarda ganin ta gudanarda wannan zaben na ran 7 ga watan gobe na Disamba, ba sani, ba sabo.

XS
SM
MD
LG