Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Peter Obi sun jinjinawa mawakiya Tems saboda nasarar da ta samu a karo na 67 na bikin ba da kyaututtukan “Grammy” da safiyar yau Litinin.
Sa’o’i bayan lashe kyautar, Shugaba Tiinubu ya bayyana nasarar da wacce ta dace.
“A madadin gaba dayan kasarmu, Shugaba Tinubu ya yabawa mawakiyar game da baiwar fasaha da Allah yayi mata, wacce ta sanya Najeriya alfahari a idon duniya har sau 2,” kamar yadda mai magana da yawun shugaban kasa Bayo Onanuga ya bayyana a sanarwar daya fitar da maraicen yau Litinin.
Tems wacce ainihin sunanta shine Temilade Openiyi ta lashe kyautar fitacciyar waka daga nahiyar Afrika mai taken “love me jeje,” inda tayi takara da mawakan Najeriya irinsu Davido da Yemi Alade da Asake da Wizkid da Lojay da kuma Burna Boy.
A cikin sakonsa na taya murna, Peter Obi yace ako da yaushe irin dimbin nasarar da matasan Najeriya ke samu a fannoni daban-daban na rayuwa na faranta masa rai, musamman ma a bangaren nishadi.”
“Don haka anan ina mika sakon taya murna ga tauraruwar kidan Afrobeat ta Najeriya, Tems, wacce ta lashe kyautar Grammy a karo na 2 a rukunin mafificiyar waka daga nahiyar Afrika,” kamar yadda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben Najeriya na 2023 ya wallafa a shafinsa na X da safiyar yau Litinin.
Dandalin Mu Tattauna