Ma’aikatar tace, jami’an tsaro ne suka tsargu da dan ta’addar, inda suka nufe shi da zummar tuhuma, sai kawai ya tada kansa a wajen.
Inda nan take ya mutu, jami’an tsaro guda 2 kuma suka dan ji rauni aka nufi asibiti da su.
Ofishin jakadancin Amurkan ya fitar da sanarwar cewa, ba wani ma’aikacinsu da ya sami rauni a harin. Sun kuma jaddada gargadin tafiye-tafiye zuwa Sa’udiyya, tare da ba Amurkawa shawarar takaita tafiyen da ba dole bane a cikin kasar.
A shekarar 2004, wasu ‘yan ta’addar da ke da alaka da ta Al-Qaida, suka kaiwa ofishin hari da bama-bamai, inda aka sami musayar harbe-harbe tsakaninsu da jam’ian tsaro Sa’udiyya, har jami’ai guda biyar da ba Amurkawa ba suka mutu a harin.