A siyasar Amurka kuma, jiga-jigan jam'iyyar Democrat suna hasashen cewa ba za'a tuhumi 'yar takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar mai jiran gado Hillary Clinton ba, saboda tayi amfani da na'urar karba da aikewa da email na kashin kanta wajen tafiyarda ayyukan gwamnatin a matsayinta na sakatariyar harkokin wajen Amurka ta farko a gwamnatin shugaba Barack Obama.
"Abunda ba zai faru ba kenan," inji senata Cory Booker daga jihar New Jersey, lokacinda yake magana jiya Lahadi cikin shirin tashar talabjin ta CNN. "wannan abu ne da a ganina zai yi wahala ainun a ce ya faru." Takwaran aikinsa Sherrod Brown shima ya furta a cikin wani shirin talabijin jiya Lahadi.
Saci fadi ya karu ainun, bayan da Mrs Clinton ta gana da jami'an FBI fiyeda sa'o'i biyu ranar Asabar. Wannan ganawar zata kasance matakin kusa da karshe kamin ma'aikatar shari'a ta fito da matsaya kan ko zata tuhumi tsohuwar sakatariyar harkokin wajen na Amurka da laifin karya doka.
"Wannan mataki ne dana yi tayi tun cikin watan Agustan bara, Mrs Clinton ta fada cikin shirin MSNBC.
Yayinda Mrs Clinton take kokarin tarfa ruwa kan batun wanda yaki-ci-yaki cinyewa,mutuminda ake sa ran zai kara da ita a zaben kasa mai zuwa watau Mr.Trump na jam'iyyar Republican, yayi amfani da sashinsa a dandalin Twitter yace "Ba zata sabu ba, ace wai hukumar FBI ba zata tuhumi Mrs Clinton ba." Abunda tayi ya karya doka. Inji Trump.