An ba da rahoton cewar Adesina ya yi tsokaci a kan yin takarar shugaban kasa a 2027 sakamakon hirar da aka yi da shi a baya-bayan nan.
Sai dai, shugaban AFDB din ya musanta rahotannin kafafen yada labaran, inda yace bai taba fadar cewa zai yi takarar shugaban kasa ba.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X yana karin haske a kan batun a jiya Laraba, Adesina yace rahotannin sun sauya wa hirar tasa ma’ana.
“Kafafen yada labaran Najeriya da dama sun sauyawa wani bangare na hirar da nayi da tashar talabijin ta Arisetv ma’ana. Abinda nace shine, “zan kasance cikin shirin hidimtawa duniya da nahiyar Afirka a ko’ina, ciki har da kasata.
“Domin kawar da shakku da adana tarihi, ban ce zan yi takarar mukamin shugaban kasar Najeriya ba,” a cewar Adesina.
Dandalin Mu Tattauna