A Fadar Vatican, Paparoma Francis ya gabatar jawabin da ya saba yi a duk shekara ga mabiya addinin Kirista a duk fadin duniya, inda ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza da Ukraine da duk wurare da ke fuskantar kalubale sanadiyar yaki.
Paparoma Francis ya kuma yi kira da a sake sauran Yahudawa da aka yi garkuwa da su yayin harin da aka kaiwa Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
A Najeriya kuma, Rabaren Lawal Ibrahim Tsanyawa, yayin wata kebabbiyar hira da Muryar Amurka bayan nasa jawabain a jihar Kano, ya ce Easter lokaci ne na gudanar da aduo’i’n ga kasa da ma yan uwa baki daya, ya kuma kara da cewa, lokaci ne na bada kyaututtuka da sada zumunci.
Rabaren yayi adu’a da Allah ya sa shugabannin Najeriya su yi adalci sannan yayi riko da hannayensu wajen kamanta wannan adalcin da saukin rayuwa.
Wasu mabiya addinin Kirista sun nuna jin dadinsu da ganin wannan rana inda suka nuna farin cikin tashin Yesu Almasihu daga matattu.
A birnin Washington, Fadar gwamnatin White House na shirin gudanar da bikin nan da ake kira ‘Easter Egg Roll.’
Ana sa ran yara mutane kusan dubu 40, za su halarci bikin a ranar Litinin, 1 ga watan Afrilu, wanda ya samo asali tun daga shekarar 1878.
Dandalin Mu Tattauna