Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fafaroma Francis Ya Koka Kan Yadda Yaki Ya Rinjayi Sakon Zaman Lafiya


Fafaroma Francis ya jagoranci taron addu'a a St. Peter's Basilica da ke fadar Vatican, Dec. 24, 2023.
Fafaroma Francis ya jagoranci taron addu'a a St. Peter's Basilica da ke fadar Vatican, Dec. 24, 2023.

Firai Minista Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadi a ranar Lahadi cewa, yakin da kasar shi ke yi da Hamas a yankin zai kasance mai tsawon gaske.

A yayin wani babban taron addu’a na ranar jajiberin Kirsimeti a St. Peters Basilica da ke fadar Vatican, Shugaban Darikar Katolika Fafaroma Francis ya bayyana cewa, matsalar-yake-yake ta yi wa sakon Annabi Isah Alaihissalam na zaman lafiya karan-tsaye a kasar da aka haife shi.

“A daren yau, zuciyar mu ta kasance a Bethlehem, inda aka sake nuna kiyayya ga Yariman zaman lafiya ta hanyar yake-yake ta yadda ya kai ga babu masaka tsinke a gare shi a duniya.” Fafaroma Francis ya ce yayin da adadin mutanen da ke rasa ransu ke kara yawa a Gaza,

Firai Minista Isira’ila Benjamin Netanyahu ya yi gargadi a ranar Lahadi cewa, yakin da kasar shi ke yi da Hamas a yankin zai kasance mai tsawon gaske.

Netanyahu ya fada a wani taron majalisar zartarwar a ranar Lahadi cewa, “bari na bayyana muku karara. Wannan zai kasance yaki na tsawon lokaci, har sai mun ga bayan Hamas da kuma maido da tsaro a yankin.”

Yayin da Isra’ilan ke ci gaba da barin wuta a kan Gaza, Falasdinawa sama da 166 aka kashe a cikin sa’oi 24 da suka wuce, abin da ya kai adadin Falasdinawan da suka rasa ransu zuwa 20, 424, a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza da Hamas ke kula da ita.

Isra’ila ta ce adadin sojojin Isra’ila da aka kashe a yakin a karshen mako ya karu da mutum 15, wanda ya kai jimullar zuwa 161 na sojojinta da aka kashe tun Isra'ilan ta kutsa cikin Gaza.

Netanyahu ya ce “wannan safiya ce mai matukar wahala, bayan wata rana mai matukar wahala na yaki a Gaza.” “Yakin yana wujijjiga mu, amma ba mu da zabi (sai dai) mu ci gaba da yakin.”

A arewacin Gaza, jiragen yakin Isra’ila sun yi ta kai hare-hare ta sama a yankin Jabalia cikin dare, yayin da a Kudancin Gaza suka kai hari a Khan Younis, mahaifa kuma cibiyar shugaban kungiyar Hamas Yahya Sinwar.

An ci gaba da gwambza kazamin fada da sanyin safiya ranar Lahadi. Isra’ila ta ce ta samu kusan cikakken iko da arewacin Gaza, inda ta kai hare-hare kusan 200 a Gaza a ranar Asabar.

Mai magana da yawun Dakarun tsaron Isra'ila na IDF, Rear Adm. Daniel Hagari, ya ce sojoji na gab da kammala samun iko a arewacin Gaza.

“Dakarun IDF na ci gaba da kai hari ta kasa a Khan Younis, kuma a lokaci guda suna shirye-shiryen fadada ayyukan zuwa wasu yankuna na Zirin, tare da mai da hankali kan kudanci,” in ji Hagari.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG