Yayin wata ganawa da manema labarai a karshen wani taron tsaro na yankin da aka yi a Kampala a jiya Litinin, Musuveni ya nuna gazawar shirin samar da zaman lafiya a Somalia.
Ya kara da cewa babban dalilin da ya sa suka tura dakarunsu zuwa Somalian shi ne a taimakawa al’umar kasar wajen samun nata sojojin, amma bayan shekaru tara, har yanzu ba a cimma wannan buri ba.
Museveni ya jaddada cewa bai ga dalilin da zai sa su ci gaba da marawa wannan shiri baya ba, wanda ya ke samun cikas saboda rashin kyakyawan tsari.
Sai dai ya ce ya gana da jami’an kungiyar ta AU da na Majalisar Dinkin Duniya, inda ya ce yana ganin akwai alamun haske a shirin samar da dakarun na Somalia a wannan karo, kuma idan ya ga akwai alamun nasara za su marawa shirin baya.
A watan da ya gabata ne Uganda ta ayyana shirinta na janyewa dakarunta daga Somalian a karshen shekara mai zuwa.