Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Me Ya Kai Firayim Ministan Israila Wasu Kasashen Afirka?


Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu da Shugaban Uganda Yoweni Museveni
Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu da Shugaban Uganda Yoweni Museveni

Firayim Ministan Israila Benjamin Natanyahu ya kai ziyara kasashen Afirka hudu dake gabashin nahiyar, to ko wannan ziyarar zata yi tasiri tare da alfanu ga kasashen da ita Israila din?

Muryar Amurka ta zanta da Farfasa Bube Namaiwa, shehun malami a jami'ar Ahmadu Diof dake kasar Senegal domin ya yi fashin baki akan wannan ziyara ta ban mamaki.

Farfasa Bube Namaiwa yace yakamata a san dalilin da ya sa Bejamin Natanyahu ya zabi kasashen hudu dukansu kuma a gabashin nahiyar. Kasashen kuma sun hada da Uganda, Kenya, Somalia da Ethiopia ko Habasha.

Yanzu da ita kasar Israila tamkar ta zama saniyar ware ce a cikin kasashen duniya saboda haka tana neman wadanda zata yi cudanya dasu. Akwai kuma dalilin da ya sa ya zabi wadannan kasashen.

Benjamin Netanyahu yana jawabi a filin saukan jiragen sama na kasar Uganda
Benjamin Netanyahu yana jawabi a filin saukan jiragen sama na kasar Uganda

Kasashen Afirka da yawa dake gabashin nahiyar Afirka suna da Yahudawa bakake, musamman Uganda da Kenya da Ethiopia wadanda ake kira Falash kuma suna da mahimmanci cikin kasashen..

Shekarar da aka yi tsananin yunwa a Ethiopia ita kasar Israila ta nemi Yahudawan su koma Israila. Dalili ke nan da ya sa yanzu akwai yahudawa bakake a Israila, su ne kuma zuri'ar Annabi Suleiman.

Dalili na biyu shi ne ta'adanci da ya shafi addinin musulunci da wasu kasashen yankin ke fama dashi. 'Yan ta'ada sun yi yawa tun ba 'yan kungiyar al-Shabab ba da suke yaduwa suna kama sauran kasashen daga kasar Somalia.

Firayim Minista Netanyahu ya yi nazari ne cewa idan Israila tana son fita daga halin da take ciki yanzu sai ta duba ta ga inda take da 'yanuwa. Ta san inda 'yanuwan nata suke amma suna cikin matsala da ta jibanci ta'adanci dake fita daga wadanda suke ikirarin suna bin addinin musulunci.

Dangane da ko ziyarar zata yi tasiri, Farfasa Bube Namaiwa yace sai dai a jira nan gaba. Amma ta fuskar taimakawa kasashen da bayanan leken asiri domin yaki da ta'adanci, nan kam ziyarar zata yi tasiri. Tana iya taimakawa kasashen ta fannin tsaro.

Babban taimakon da ita Israila zata samu shi ne shiga kawance ta samu kasashen da zata dinga hulda dasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:06 0:00

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG