Babban jami’in ‘yan sanda Joseph Boinnet yace ‘yan sanda dake wurin, sun tarar an harbe mutane shida har lahira. Ana kuma kan farautar ‘yan ta’addan.
Ana kyautata zaton farin kaya hudu da masu gadi biyu dake dauke da makamai, suna daga cikin mutanen da aka kashe. A kalla fasinjoji biyu kuma sunji rauni.
Kungiyar al-Shabab dake makwabciyar kasar Somalia, sun kai irin wadannan hare haren a lardin arewa maso gabashin Kenya dake fama da talauci.
Kwana guda kafin wannan harin na yau, a kalla mutane ishirin suka mutu a wata fashewa da ta auku a gefen hanya da ta shafi wata motar safa a Somalia.
Kungiyar al-Shabab da ake alakantawa da Al-Qaida, ta kashe dubban mutane tunda ta fara ta’addanci shekaru goma da suka wuce.