Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalibai A Kenya Sun Kirkiro Naurar da Zata Taimakawa Mata Masu Juna Biyu da Jarirai


Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta
Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta

Wasu ‘yanjami’ar birnin Nairobi dake kasar Kenya sun kwashe shekaru biyu domin samar da wata naura da zata inganta rayuwar mata masu juna biyu da kuma lafiyar jarirai.

Wadanda suka samar da wannan naurar dai wasu dalibai ne da ake kira Joel Kabete shi da takwaran sa, da suke aji guda a jamia’ar.

Kuma sun kwashe shekaru biyu ne domin kirkirar wannan naurar wadda take agazawa jariri da nunfashi bayan haihuwar sa ko kuma lokacin da ake kokarin fidda shi daga mahaifa.

Ita dai kasar Kenya sau tari tana sayo kayayyakin aiki na asibiti ne daga kasashen waje.

Misali, irin wannan naurar ana sayar da ita a kasar waje akan kudin Amurka dala dubu 2, amma wannan da suka kirkira za’a iya sayarakan kwatankwacin dala dari 5.

Joel, daya daga cikin wadanda suka kirkiro wannan naurar wanda yake kwas din injiniya, yace sunyi anfani ne da kayayyakin cikin gida domin kyera wannan naurar .

Yace wannan zata zame tamkar wata fadakarwa ce domin ko ana iya anfani da kayayyakin gida domin kyera wata naura da zata anfani yaraharma da al’umma baki daya.

Raphael Osoro daya dalibin da suka kirkiro wannan naurar tare shine ya zayyana ta,wanda yace ya kwashe watanni 6 yana nazarin zayyana wannan naurar.

Ita dai wannan naurar mai fitar da launin shudi daga cikinta zata rage yawan wani abu dake taruwa a hantar jariri wanda sau tari yake haifar da cutar shawara

XS
SM
MD
LG