A wani taro da Kungiyar masu sarrafa Biredin ta kasa ta gudanar a birnin tarayya Abuja, shugaban kungiyar na kasa Alhaji Zubairu Abubakar Shu’aibu, ya koka bisa tsadar sinadaran hada Biredin abin da yace shine ke haddasa rufe gidajen Biredin.
Alhaji Zubairu, ya kara da cewa gwamnati kadai itace tafi gidajen Biredi samar da ayyukan yi, ya kuma ce idan har farashin kaya bai sauko ba to zasu koyi kara farashi da zarar an kaya sun tashi.
A baya dai tsohon shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan, ya shawarci masu sarrafa Biredi da su fara amfani da fulawar garin Alabo, kasancewar tashin farashin fulawar Alkama. Shugaban kungiyar masu Biredi na jihar Jigawa, Yunusa Mohammed, na ganin idan har za ayi Biredi na gaskiya dole ne ayi amfani da fulawar Alkama. Ya kuma kira ga gwamnati da ta kalli wannan lamarin kasancewarta barazana ga matasa masu aikin yi.
Shima shugaban kungiyar reshen jihar Inugu, Chief Sunday Ekam, ya gabatar da kasida kan musabbabin matsalar, inda yace farashin Alkama ne ke haddasa farashin fulawa a kasuwannin duniya, farashin Dala kuma shine ke haddasa farashin Alkama, kan wannan lamari babu wani abu da gwamnati zata iya yi yanzu, sai dai gwamnatin ta zaburar da noman Alkama a cikin kasa.
Domin karin bayani.