Shugaban masu rinjaye a majalisar Ali Ndume yace kin amincewa da bukatar shugaban kasa da majalisar tayi ya bashi mamaki.
To amma Sanata Ali Ndume tamkar yayi amai ya lashe ne yayinda ya dorawa ofishin shugaban kasa laifi akan dalilin da ya sa majalisar bata biya masa bukata ba. Yace wasikar da shugaban ya aiko masu bata kunshi cikakkun bayanai ba. Yace babu bayanan da suka kamata a hada a ba kwamitin da zai yi nazari akan bukatar.
Wasikar shugaban kasa bata bayyana inda za'a ciwo bashin ba, kazalika shekaru nawa za'a yi ana biyan bashin da kuma kason da za'a biya kudin ruwa. Baicin wadannan yakamata a san sharudodin dake tattare da bashin. Ali Ndume yace bata yiwuwa majalisa ta amince da bukatar ido a fufe.
Ali Ndume yace bashin ba na cikin gida ba ne. Daga waje za'a karboshi kuma yana iya kawo matsala irin wadda ya sa kasar ta sha da kyar yayinda ta ciwo bashi daga kasashen waje.
Sanata Ita Enang mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin majalisa yace sun ji korafin sanatocin kuma zasu yi iyakar kokarinsu su bada duk takardun da suke bukata.
Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.