'Ya'yan kungiyar dake jihar Filato sun bukaci hukumomi da su sako mambobinsu guda arba'in da hudu da ake tsare dasu.
Kungiyar na zargin cewa cikin wadanda aka tsare har da kananan yara da mata dake jego da masu juna biyu da 'yan makaranta.
A taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Jos babban birnin jihar Filato tace makonni ukku ke nan da jami'an tsaro suka kame wasu mutanensu kuma duk kokarin da kungiyar tayi domin a sakosu ya cutura.
Shugaban kungiyar Dr. Ibrahim Suleiman Jahun yace sun kira taron manema labarai ne domin su sanarda duniya halin da suka tsinci kansu a ciki. Bukatarsu shi ne a sako masu mutane domin acewarsa ba laifi suka yi ba amma a kotu an ce wai sun tada hankali.
Baicin bukatar a sako masu mabobinsu dake tsare kungiyar na neman a biyata diya akan kayansu da wai aka lalata ko aka kone. Sun kira kuma da a daina tunzurasu domin su basu tunzuri kowa ba, kuma "har abada ba zamu taba hankalin kowa ba",inji Dr Jahun.
Amma kakakin rundunar tsaro ta musamman a jihar Manjo Ikedichi Iweha yace wadanda rundunar ta kama a ranar da suke bikin ashura baki ne da suka fito daga Bauchi da Gombe da Saminaka da Kafanchan da dai wasu wuraren. Su ne suka kama suka kuma mikawa 'yansanda.
Mai ba gwamnan jihar shawara kan harkokin manema labarai Daniel Manja yace gwamnati ta dakatar da kungiyar ne a jihar domin tabbatar da tsaro.
Gwamnan jihar ta Filato Simon Lalon yace gwamnonin arewa zasu yi taro da shugabannin kungiyar ta shiya domin tabbatar da zaman lafiya.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.