A wurin ganawar al'ummar Niger Delta sun gabatar da bukatunsu yayinda shi kuma Shugaba Buhari yayi masu gargadi akan abubuwan da ake bukata domin nasu bukatun su tabbata.
Shugaba Buhari yace tilas ne sai akwai zaman lafiya da kwanciyar hankalin sannan za'a samu wadata da masu saka jari su shigo kasar. Shugaban yace amma muddin ana tada zaune tsaye babu wata gwamnati ko a wacce kasa ce da zata iya gamsar da al'ummar kowace yanki.
Malam Garba Shehu kakakin shugaban Najeriya dake fadarsa yayi karin haske dangane da bukatun da su al'ummar Niger Delta din suka gabatarwa shugaban.
Malam Garba Shehu yace abubuwan da 'yan Niger Delta ke bukata basu da banbanci da bukatun sauran 'yan Najeriya. Suna neman a gina masu tituna da tasoshin jiragen ruwa da fadada tekunansu ta yadda manyan jiragen ruwa zasu shiga yankunansu saboda inganta tsaro da samar ma matasa abun yi domin a dakile satar mutane.
'Yan Niger Delta din sun bukaci a dinga sasu a harkokin man fetur, ana damawa dasu. A basu damar hakan man fetur ko dama za'a bar gwamnatocin jihohinsu su yi. Sun kuma kira a sake duba yadda ake rabon arzikin kasa musamman kudaden da kasar ke samu daga man fetur domin suna bukatar su ci moriyar abun da Allah ya sa a kasarsu.
Amma a nashi bangaren Shugaba Buhari yace bukatar farko ita ce a zauna lafiya illa iyaka. Idan babu zaman lafiya babu arzikin da zasu iya samu. Yace zaman lafiya ne zai jawo masu saka jari na kusa da na nesa.
Shugaba Buhari ya gayawa shugabannin cewa barnar da ake yi a yankinsu ta isa. A matsayinsu na shugabanni su tashi suyi maganin tashin hankali kada su dinga cewa duk wata matsala daga Abuja ake haddasata. Yace su je su ga abun da zasu iya yi a kai. Yace idan suka gaza babu yadda za'a ga martabarsu a matsayinsu na shugabanni.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.