Hamshakin attajirin nan na jam'iyyar Republican dake neman shugabancin Amurka ya soma kiran masu goyon bayansa da su soma tara kudin yin kemfen.
Wannan kokari ne yake yi domin ya cike gibin kudi dake akwai tsakaninsa da Hillary Clinton wadda ake kyautata zaton ita ce zata lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar Democrat.
Shi dai Trump mai son cika baki, bai taba shiga siyasa ba, sai wannan karon. Ko da ya fito kusan su goma sha shida suka fito daga jam'iyyarsu kowannensu na zaton shi ne zai zama zakara. To amma abun mamaki sai gashi Trump din ne ya rage kuma shi ne kan gaba.
Daren jiya ne ya kaddamar da wata liyafar cin abincin yamma a birnin Los Angeles inda duk wanda ya kasance wurin zai sayi kawanon abinci daya akan kudi dala dubu ashirin da biyar, ko $25,000.
Tun farko dai da ya fito Trump ya sha cika baki da cewa shi ba zai nemi kudin kowa ba domin babu wanda zai sayeshi. Yace baya bukatan taimakon manyan attajirai da kan tara kudi ma dan takaran shugaban kasa.
Tun lokacin da ya fara kemfen dinsa kawo yanzu Trump ya bada lamunin dala miliyan 43 ma kamfen dinsa cikin shekara daya. Ya karbi 'yan kananan taimako daga wasu mutane amma ya ki na attajirai 'yan uwansa.
A cikin wata yarjejeniya da ya cimma da shugabannin jam'iyyar Republican ya bukaci su tara masa dala biliyan daya domin yakin neman zabe.
Yanzu dai alkalumma sun nuna Hillary Clinton na gabansa nesa ba kusa ba da tara kudade. Yayinda Trump ya tara dala miliyan 59.4 ita kuwa ta tara miliyan 300. Ko watan jiya ta tara miliyan 30 shi ko miliyan biyu kawai ya samu