Wasu kungiyar rajin sa ido ga shari’a da ake kira Judicial Watch sun kai Hukumar Harkokin wajen Amurka kara game da shiga sakonnin email din da Hillary din ta aika a lokacin da takje Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka.
Inda suke kalubalantar Hukumar da cewa bata saki dukkan bayanan da aka nemi su yi ba a karkashin dokar ‘yancin musayar bayanai akan tsoffin ma’aikatan da suka yi aiki da Hillary wajen kirkirar shafin sakonnin email dinta ba.
Alkalin gunduma Emmet Sullivan ya fada a jiya Laraba cewa, “zai iya yiwuwa in bukatar hakan ta taso a kira Mrs. Clinton, don yin bayanin yanayin da ya bada damar da har ma’aikatar Harkokin Wajen ta yarje mata amfanin da email din kashin kanta wajen aiki ofis.
Tsohuwar Sakatariyar ta sha bayyana cewa bata yi wani laifi ba, tana cewa ta yi amfani da shafin email daya na kashin kanta da kuma na aikin ofis saboda samun nutsuwa. Masu sukar Clinton irin su abokin hamayyarta Donald Trump ya soketa da cewa ta sa tsaron Amurka a cikin hatsari.