Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, jiya Laraba, ya caccaki Hillary Clinton, yace abokiyar takararsa ta jam'iyyar Democrat, "tana iya zama mutuniyar da ta dara ko wani dan takara da ya taba neman shugabancin Amurka rashin gaskiya, ita kuma Clinton ta maida martani cewa, zarge zargen nasa ba wani abu bane illa karairayi."
A cikin jawabin da yayi jiya a birnin New York yayinda nagoya bayansa suke sowa, Trump ya zargi tsohuwar sakatariyar harkokin wajen na Amurka cewa, ta goyi bayan manufofin Amurka a kasashen waje wadanda suka haifarda "kashe kashe da lalata dukiya, da janyo ta'addanci" yayinda take rike da wannan mukamin tsakanin shekara ta 2009-2013, sannan daga bisani ta arzurta kanta da miliyoyin dala ta wajen gabatar da jawabai da ake biynata da wadannan kudade.
Sukar da Trump ya yiwa Clinton, ta zo ne kwana daya bayanda tayi kaca-kaca da ikirarin cewa shi mutum ne daya kware ta fuskar kasuwanci, ta ambaci matakan da ya dauka har sau hudu na ayyana kamfaninsa a zaman wanda hanun jarinsa ya karye.