Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ce dai tayi nasara da babban rata a zaben na jiya Talata wanda aka yi a nan Washington DC.
Tun farko dai ta samu kuriun da ake bukata wanda ya nuna cewa itace zata zama ‘yar takar jamiyyarsu ta Democrat.
Yanzu haka Hilary da abokin karawarta na jamiyyar tasu Barnie Sanders sun tattauna a jiya jim kadan da kammala zaben, domin tattauna batun babban taron da za ayi.
Sanders yayi alkawarin samar da yanayi mafi yada akidar sassauci da aka taba samnu a jamiyyar democrat.
Sanders yana magana sailin da yake amsa tambayoyin manema labarai yana cewa jamiyyar su ta Democrat tana tare da ma'aikata, yace tun da jimawa ne yakamata ace an sauya wasu manufofin jamiyyar tasu.
Mutane dai masu ra'ayin sassauci sunsha fada cewa jamiyyar ta faye sakwa-sakwa a wasu al’amura, suna cewa sau tari sai kaga tana samun daidaito da jamiyyar Republican, wanda hakan na nuna cewa dukkan su dan juma da dan jumai ne.
Clinton bata bayyana abinda ya wakana tsakanin ta da Sanders ba a tattaunawar su jiya Talata, sai dai jami'an kanfe dinta sun bayyanawa kanfanin dillacin labarai na Reuters cewa tana kokarin ganin yadda zasu hada karfi da karfe ne domin taka wa Donal Trump burki wajen zamowa shugaban Amurka.