Dan takarar shugabancin Amurka karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump, yana zargin cewa wasu 'yan jam'iyyar Republican suna kokarin yi masa zagon kasa ga zamansa dan takarar jam'iyyar a lokacin da jam'iyyar zata yi babban taronta cikin watan gobe.
Wasu wakilai a da zasu je babban taron jam'iyyar suna son ganin an sauya dokokin taron ta yadda wakilan zasu zabi wani mutum daban, domin kalamansa sun saba da matsayar da jam'iyyar ta bada misali abubuawa da ya fada kan mata, da musulmi da 'yan kabilar Latino.
Ko a jiya Trump sai da ya sake cewa, banda batun hana musulmi shiga Amurka, akwai bukatar Amurka ta fara sa ido kan musulman da suke Amurka.
A halin da ake ciki kuma, tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary da mijinta tsohon shugaban kasa Bill Clinton suna cike da murnar samun wani jika. 'Yarsu Chealsea ta haifi da namiji ranar Asabar.