Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada Shamsedeen Ogunjimi a matsayin sabon babban akanta na tarayyar kasar bayan wani tsarin zabe mai tsauri.
Sanarwar da mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, yace nadin da aka amince da shi a yau Talata, zai fara aiki ne a ranar 7 ga watan Maris din da muke ciki, a ranar da me rike da mukamin a halin yanzu Oluwatoyin Madehin zata yi ritaya.
An fara ambata Ogunjimi mai shekaru 57, a matsayin wanda zai maye gurbin madehin a watan Disamban da ya gabata.
Mamba ne a cibiyar kwararrun akantoci ta Najeriya da kuma takwararta ta kwararrun masana haraji.
Dandalin Mu Tattauna