Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tazarar Da Ke Tsakanin Hillary Clinton Da Donald Trump Na Kara Tsukewa


Donald Trump da Hillary Clinton,
Donald Trump da Hillary Clinton,

Hillary Clinton da Donald Trump basu yi kwauron baki ba a yayin da ratar dake tsakanin su a kuri’ar gwaji ke kara tsukewa, dukkan su Yan takarar na kokawar samun damar cin zaben dake kara matsowa.

Clinton tayi jawabi a ralin da ta gudanar a Garin Dade dake Florida a yunkurinta na maida hankalin kan Trump bayan kwashe kawanaki da fama da da sabon binciken Email da hukumar FBI suka dawo dashi akanta.

Ta futo tana kaffa kaffa da ambaton Trum kai tsaye amma ta taso da wasu tsofafin kalamai da yayi inda tace “ Ya dade yana kaskantar da wulakantar da mata”.
“Zan so ace inyi Magana kan wasu abubuwan a wurin nan amma dole myi Magana akan abninda a zahiri ya kona mana rai, kuma da ciwo saboda abin dubawa ne, ba zamu iya dauke kanmu daga kaiba.”

Tsphuwar mai rike da Kambun mata na Duniya Alichia Machado wacce Trump a baya ya kira da Tayi kiba wacce ta kasance cikin cece kuce da Trump a watan da ya gabata ce ta gabatar da Clinton a jiya Talata da daddare a wajen taron.

A yayin da Clinton ke sukar Trump akan irin halayyarsa , Shi kuwa Trum ya maida hankaline akan gazawar Tsarin harkar Lafiya ta Obama Care wacce ake sa ran wasu daga cikin tsare tsaren zasu samu hauhawar farashi da kusan kaso 25 a shekarar 2017.

Trump yace” Hillary Clinton tana son ta fadada Obama Care zata sa ta kara tsada ta na son ta saka gwamnati ta kula da harkar lafiya kacokan” A yayinda yake ralin sa a Jihar Pennsylvania a Jiya ya kara da cewa” Idan cgyara ko canza Obama care ba zamu lalata Tsarin harkar lafiya a Amurka har’abada. Yana daya daga cikin abubuwa masu muhimmanci da yasa dole muci zabe a ranar 8 ga watan Nuwanba.

XS
SM
MD
LG