Wani dan majalisar Kula da yan gudun hijira mai suna Wolfgan Gressmann yace “A yanzu muna tsimayin abu mafi muni da zai iya faruwa” rayuwar fararen hulu na kusan miliyan 1.5 na cikin mummunan hadari, sannan kuma babu tabbas a makomar Iraqi.
Kungiyar tace dubunnan fararen huluna ne suka gudu daga birnin, da yawa daga cikin su tuni sun mutu sakamakon Yan kwanton bauna ko kuma nakiyoyi. Wadanda suke a cikin birnin na bukatar abinci, ruwa da kuma magunguna, rashin wadan nann abubuwan a yayin da fadan ke kara tsamari ya kara wa masu agaji sukai kayan taimako.
Dakarun Iraqi dai suna wajen Birnin a ranar Talata , Sati biyu bayan fara shirin karbo birnin na biyu mafi girma a Iraqi wanda yakai shekaru biyu a hannu yan kungiyar Da’esh.
Wani Janar a cikin dakarun Iraqi yace sun kwato wani gidan Talabijin a ranar Talata kafin Guguwar Yashi ta dakatar da shirin suna ranar.
A yau Laraba dai dakarun sun ja tunga a ganuwar gabashin Birnin yayin da zafi da kuma Hadari ya takaita hangen na’urar Drones dinsu da sauran Jiragen sama.
Kungiyar dillancin Labarai ta Associate press ta rawaito cewa Birgadier Janar na Iraqi Haider Fadhil yace a yanz dai basu yi wani shirin cigaba da kai harin ba a yau Laraba sakamon rashi kyawun yanayi.