Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren MDD Ya Kori Kwamandan Rundunar Sojojin Kiyaye Zaman A Sudan Ta Kudu


Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon
Babban Sakataren MDD Ban Ki-moon

Biyo bayan rahoton wani bincike da aka gudanar aka ayyukan rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya dake Sudan Ta Kudu Ban Ki-moon ya sallami kwamandan sojojin bisa ga zargin gazaw wajen kare fararen hula da ma'aikatan bada agaji

Wani binciken cibiyoyi masu zaman kansu da aka gudanar a kan tarzomar da ta barke cikin watan Yulin da ya gabata a Sudan ta Kudu ya gano cewar rundunar kwantar da tarzoma ta Majalisar Dinkin Duniya ko MDD da sojojin kiyaye sulhu sun gaza wurin kare fararen hula da ma’aikatan agaji.

Wani kakakin MDD yace babban Sakataren MDD Ban Ki-moon ya bukaci a canza komandan sojojin zaman lafiyar na MDD dake aiki a Sudan ta Kudu.

Wannan fada tsakanin sojojin gwamnatin shugaba Salva Kiir da rundunar masu biyayya ga madugun yan adawa Riek Machar ya barke ne a ranar takwas ga watan Yuli kusa da fadar shugaban kasar. Wasu rahotanni sun ce mutanen da aka kashe a rikicin sun kai 300.

MDD dai tana da sojoji sun kai 14,000 dake Sudan ta Kudu. A birnin Juba, akwai sojojin kasashen China da Ethiopia da Nepal da kuma Indiya dake aiki a wurin a lokacin tarzomar.

XS
SM
MD
LG