Tawagar dai ta ziyarci wannna kauye na Dalori inda suka ganewa idanunsu irin yadda wannan mahara sukayi barna, da kuma jajantawa mutanen wannan kauye, harma da yin addu’a ga wadanda suka raunata.
Bayan ziyartar wannan gari ne dai sakataren gwamnatin tarayya Injiniya Baba Chir David, ya yiwa al’ummar wannan gari jawabi, inda ya gaya musu cewa shugaban kasa ne ya aiko su domin yiwa mutanen yaje.
Wakilin Muryar Amurka ya lura da wasu ‘dai ‘dai kun jama’a a kauyen wanda ke zaune bakin bishiya, yayinda kusan dukkannin gidajen dake wannan kauye sun kasance tamkar kango. Wasu mazauna garin sun bayyana halin da suke ciki tun bayan harin, inda sukace matsalar abinci da ruwan sha ke damunsu gashi an kone musu gidajensu.
Tawagar dai sun ziyarci asibitoci da ke cikin garin Maiduguri, wanda suka hada da asibitin koyarwa da na kwararru don jajantawa mutanen da if’tila’I ya shafa. Sai dai babu wani tallafi ko kuma alkawari da wannan tawaga suka yi wa mutanen.