Da take kaddamar da shirin, shugabar jami’ar Amurka a Najeriya Dr, Magee Ensign ta ce yara dubu ashirin da biyu ke cin gajiyar shirin inda jami’ar ke anfani da sabbin dabarun koyarwa, ciki harda ta kafar radiyo.
Wakilinmu Sanusi Adamu ya ba da rahoton cewa cibiyar raya kasashe masu tasowa ta Amurka tare da hadin gwiwar kasar Ireland sun yi alkawarin fadada shirin zuwa wasu sassa na Najeriya da zaran kashi hamsin bisa dari na daliban sun iya karatu da lisafi ciki watanni shida.
Domin inganta shirin koyar da karatu da lissafi jami’ar Amurka a Najeriya ta kafa cibiyoyin karatu 750, akwai kuma malamai 750 cikin ‘daliban jami’ar da suka sadaukar da kansu karkashin wannan tsarin, haka kuma jami’ar ta wallafa littattafai sama da hamsin cikin harsuna masu saukin fahimta ga daliban.
Baya ga amfani da harsuna mafi saukin fahimta ga daliban da kuma koyar da yara yan shekara 7 zuwa 16 sana’o’I domin dogaro da kai, jami’ar na amfani da radiyo wajen koyarwa.
Saurari cikakken rahotan Sunusi Adamu daga Yola.