Rundunar tana anfani da jiragen ne sabili da dalilai guda biyu kamar yadda shi Group Captain Sami Wiwa ya yiwa Muryar Amurka bayani.
Jiragen na tayasu tattara bayanan siri da kuma kai farmaki daga nesa saboda suna dauke da manyan makamai.
Saidai alamar tambaya nan itace tunda suna anfani da jiragen suna tattara bayanan siri me ya hanasu gano 'yan Boko Haram yayinda suka kai hari Dalori a jihar Bono. Wiwa yace su ma 'yan Boko Haram ba barci su keyi ba. Suna da nasu dabarun.
Amma mayakan sun takaita kuma sun takura 'yan Boko Haram din saidai yakin ba abun da za'a iya kawo karshensa ba ne rana daya.
Dr. Muhammad El-Nur Dengel na jami'ar Maiduguri kwararre ne akan harkokin tsaro yace sai an iya tantance inda 'yan ta'adan suke ne za'a iya yin anfani da kuramen jirage. Idan ba haka ba babu yadda jiragen zasu tantance Boko Haram.
Amma wani tsohon hafsan sojan sama mai murabus Aliko El-Rashid yace kuramen jiragen da Najeriya ke anfani dasu ba masu tattara bayanai ba ne, na yaki ne, farmaki kawai zasu iya kaiwa.
Ga karin bayani.