An dai kirkiro wannan kungiyar WOWWI (women without walls initiatives), biyo bayan rikice rikice da akayi ta fama da su a jihar Plateau, da niyyar sasanta tsakanin al’umma da samar da kyakykyawan zamantakewa.
‘ya ‘yan kungiyar dai sun hada da mata musulmi da krista dake ayyuka da dama musammam a yankunan da a baya ake samun tashin hankali da suka hada da unguwannin Gangare da Bauchi road da Unguwar Rukuba da Gada Biyu da Bukur a cikin garin Jos. Sai kuma kananan hukumomi Riyom da Barikin Ladi da Wase.
A cewar shugabar kungiyar Madam Esther Ibanga, tace kasar Amurka ta yaba ne da ayyukan kungiyar ta kuma amince ta tura wasu ‘ya ‘yan kungiyar zuwa kasar Nijar domin su horas da iyaye wasu dabarun koyar da yara dabi’u masu kyau.