Rundunar sojan Najeriya tace zata ci gaba da martaba zaman tattaunawar da ake, sai dai kuma idan tattaunawar ba ta sami nasara ba, rundunar tace zata dauki matakan da suka dace. A cewar maigana da yawun hedikwatar rundunar sojan Najeriya Birgediya Janal Rabe Abubakar, suna sane da tattaunawar da ake tsakaninsu da gwamnatin tarayya domin ganin an samu sulhu.
Haka kuma fadar shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari, tace ta bayar da lokaci ne kawai ga ‘yan yankin na Niger Delta domin a cimma nasarar wannan tattaunawa, A cewar maigana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, Buhari baya so yayi garaje kan wannan harka, domin an san farkon yaki amma ba a san karshen shi ba, ko kuma wa zai shafa.
A cewar wani dan kungiyar ‘yan bindigar Niger Delta Main, yace tattaunawar da ake yi a yanzu abu ne mai kyau sai dai kuma wadanda ake tattaunawar da su babu wani abu da ka iya biyowa baya a ganinsa, don ba a kama hanyar da ta dace ba.
Saurari cikakken rahotan Lamido Abubakar Sokoto.