Dan Majalisar Wakilai Gudaji Kazaure, ya nuna rashin goyon bayan lamarin inda yace, “A dakatar da Abdulmumin bamu goyi ba yaba, saboda bamason abin da zai tayar da futuna da zata tayarwa da mutane hankali a cikin gida, dakatar da shi bashi bane magani ba, domin sanda aka dakatar da shi sannan zai fara rigima.”
Majalisar dai ta dakatar Jibrin bayan da kwamitin ladabtarwa ya gabatar da rahotan nuna Jibrin yaki bayyana gaban kwamitin don amsa zargin zubarwa Majalisar mutunci kan zargin aringizo ko cushe a kasafin kudi.
Sai dai tsohon ‘dan Majalisar Wakilai Ibrahim Bello, yace Jibrin din ne ya jawo kansa wannan hukunci, inda yace shine ya kamata ya bayyana gaban kwamitin ya sanar da su abin da ya faru tare da hujjojinsa domin abi ba’asi, hakan zai sa ya karawa kansa daraja kuma ya nuna cewa yasan abin da yake.
Shima dattijo mai wa’azin Islama sheik Yakubu Musa Hassan Katsina, na da ra’ayin Majalisar tayi gaggawar ‘daukar matakin da hakan zai haddasa ayar tambaya, ya kuma ce yakamata a bari shari’a ta yi aiki, a kuma tabbatar da cewa makaryaci ne shi domin yayi kage, hakan zai sa ‘yan Najeriya su fahimci waye ke da gaskiya.
Abdulmumin Jibrin dai yace wannan dakatarwar ba ta bashi mamaki ba, inda yace “nasan cewa akwai wani shiri da suke hakan yasa nace ba zan bata lokaci na naje gaban wannan kwamitin ba. duk abin da suka yi aikin banza ne domin bashi da wani amfani, takardar da aka kai gaban Majalisa kamar takardar tsire ne bata da wani amfani bata da daraja kuma kotu zata karyata.”
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.