Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Jihar Taraba Yan Gudun Hijira Na Neman A Mayar Dasu Garuruwansu


'Yan Gudun Hijira
'Yan Gudun Hijira

Yan gudun hijira a jihar Taraba na ci gaba da kokawa game da halin da suke ciki ayanzu, inda suka nemi da a gaggauta mayar da su yankunansu da suka fito.

Yan gudun hijirar dake zaune a wani sansani da aka tanadar musu a Mutum Biyu, sunce suna cikin mawuyacin hali na rashin ababen more rayuwa ta fuskar abinci da kuma kiwon lafiya. Sansanin dai yana kunshe ne mutane a kalla Dubu 1,691 wadanda tashe tashen hankula masu nasaba da addini da kuma kabilanci ya ‘dai ‘dai ta musamman daga Kudanci da kuma tsakiyar Jihar Taraba.

A cikin wannan sansanin ‘yan gudun hijira sunce rayuwa sai a hankali, domin sauro na takura musu da rashin wadataccen gurin kwanciya. Ko da yake sun sami ‘dan tallafi daga gwamnatin Tarayya, to amma fa sunce yanzu bukatarsu itace su koma gida domin gyara muhallansu.

Shugaban Sansanin na Mutum Biyu Amadu Saliyo, yace su dai suna wannan sansani ne domin basu da zabi, kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta taimaka wajen samar da hanyar da za a mayar da su garuruwansu.

To sai dai kuma gwamnatin jihar ta zargi ‘yan gudun hijirar ne da neman nokewa duk kuwa da cewa yanzu hankula sun fara kwantawa a wasu yankunan da aka samu tashin hankali.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00

XS
SM
MD
LG