Kalamun na Dino Melaye ya jawo zullumi tsakanin makiyaya da shugabannin kungiyarsu ta Miyetti Allah.
Melaye yayi furucin ne lokacin da kwamitin Abuja ya gayyaci ministan Musa Bello akan lamuran birnin. Baicin a kama saniyar da ta ratsa birnin kamar umurnin da Melaye ya bayar ya kuma ce a ci tarar mai ita nera dubu hamsin.
Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah reshen Abuja Abubakar Suleiman yace basu ji dadin yadda Melaye yayi anfani da kalmomi masu tsanani haka ba. Sun bukaci Melaye ya je gidan rediyo ya karyata kalamun da yayi. Shi ma ministan Abuja Fulanin sun umurceshi ya kirawo shugabannin Fulani su zauna dashi su tattauna akan shigo da shanu cikin gari.
Abubakar Suleiman yace su din sun damu da yadda mutanensu ke shiga birnin da shanu. Zasu gargadesu su koma inda ba cikin gari ba ne saboda gwamnati tayi masu alkawarin dazuka. Yace su Fulani sun rsa inda zasu sa kawunansu saboda babu daji.
Abubakar Sani mai taimakawa ministan Abuja kan labaru yace dokar da ta hana shanu zirga zirga kan tituna Abuja tana nan kuma zasu yi aiki da ita. Ministan ya umurci jami'an tsaro da su tabbatar da dokar tayi aiki.
Abubakar Suleiman ya bukaci Melaye ya janye kalamun da yayi domin wai su Fulanin suna shirin kaishi kara kotu.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.