Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan Najeriya Sun Dage Sai Sun Ga Bayan Rundunar SARS


Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja.
Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja.

‘Yan Najeriya a jihohi da dama sun dage da kamfen din neman lalle rundunar ‘yan sanda ta soke sashen ta mai yaki da ‘yan fashi “SARS” don samun su da cin zarafin al’umma, wuce gon da iri dama kashe wasu ba tare da gurfanar da su gaban kotu ba, kuma kan tuhumar da ba a kammala bincike ba.

Duk da sanarwar da babban sifeton ‘yan sandan Muhammad Adamu ya fitar da ke baiyana dakatar da sintirin ‘yan SARS da takaita aikin su ga yaki da ‘yan fashi, hakan sam bai gamsar da jama’a ba da ke son a soke su gaba daya.

Hatta mataimakin shugaban kasar Najeriya Yemi Osinbajo, ya nuna bacin rai ga aiyukan rundunar SARS bayan kashe wani matashi a Lagos, inda ya gana da babban sifeto da umurtar sa ya yi garambawul ga rundunar don ta dace da tsarin kare hakkin ‘yan adam.

A ranar Lahadi da ta gabata shaharerren mawakin nan na Najeriya Davido, ya gaiyaci mazauna Abuja su raka shi don gudanar da gangamin neman soke rundunar SARS.

Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja
Masu Zanga-Zangar Sai An Soke Rundunar SARS a Abuja

A baya, an sha yin garambawul ga rundunar amma ba wani sauyi da a kan gani sai ma sabon salon muzgunawa jama’a.

Ofishin ‘yan sandan SARS na Abuja, a cike ya ke kullum makil motoci tamkar tashar mota na mutanen da a ka kama ko kuma masu zuwa don neman belin ‘yan uwan su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG