Biyo bayan rahotannin gano yaran da aka sace a jihohin arewacin Najeriya musamman jihar kano, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya gudanar da taron zauren VOA na wata-wata don tattaunawa kan yaki da yawaitar satar yara da sayar da su a wasu jihohin kudu maso gabashin Najeria.
A taron wanda ya samu halartar manyan baki maza da mata daga ciki da wajen Abuja an cimma matsaya cewa kalubalen daga wasu miyagun iri ne ba wai batun kabila ko addini ba.
Igwe Martins mai kamfen din zaman lafiya kuma dan kabilar Igbo ya ce akan samu irin wadannan bata gari a cikin ko wace kabila, amma kai tsaye a hukunta masu laifi don kafa misali ta yadda wani ba zai yi sha'awar aikata irin wannan muguwar dabi'a ta satar yara ba.
Shi ma shugaban rundunar adalci daga jihar kano, Abdulkarim Dayyabu, ya jaddada muhimmancin dawo da martabar sarakuna ko hakimai zuwa masu unguwanni don sanin shige da ficen jama'a wajen shawo kan matsalar.
Jami'i a sashen hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda Abuja, CSP Baba Inna, ya ce rundunar na iya bakin kokarinta wajen gano inda matsalar take tare da jan hankalin iyaye wajen sa ido akan yaran su.
Sauran mahalarta taron sun nuna jin dadin su ganin yadda aka basu dama wajen bayyana ra'ayin su tare da yin jawabai da kuma tambayoyi don samun mafita game da lamarin na satar yara.
Saurari cikakken rahoton wakiliyarmu Hauwa Umar daga Abuja:
Facebook Forum