Kusan watanni uku bayan da Gwamnatin Tarrayar Najeriya ta rufe iyakokinta da makwabtanta da suka hada da Nijer, Benin, Kamaru da Chadi, al'amura na cigaba da kai wa mazauna na Nijer da Najeriya da ke wadannan wurare karo, ganin cewa, kasuwanci ya tsaya.
Alhadji Sani mai K7 shi ne shugaban kungiyar ‘yan kasuwa na Birnin N'Konni a iyakar Birnin N'Konni ta jahar Tawa a Nijar da Illela a jahar Sakkwaton Najeriya, inda manyan motoci na dakon kaya na kamfanin Dan Gote da sauran su sama da 500 ne ke jibge an hana su shiga Najeriya sama da watanni 2 da rabi. Daya daga cikin direbobin da ke wurin, mai suna Abdul Fata'u Kware ya yi bayanin halin da suke ciki a bakin wannan iyakar, inda ya ce, ya tsallaka daga Nijar zuwa Najeriya, inda ya ajiye motarsa daga nesa da iyaka, sannan ya bada takardun sa na ECOWAS ko CEDEAO aka buga musu sitam ko Kashe a lokacin fita daga Nijar da lokacin shiga da dawowa daga Najeriya da na shiga ta kasa kuma dawo ta kasa.
Akwai dan kabu - kabu na Najeriya da bai so ya bayyana sunansa ba, ya shigo Nijar, ya yi bayanin matsalolin da su ke fuskanta tun lokacin rufe wannan iyakar.
Alhadji Usman Giwa, wani dan kasuwa daga Illelar a jahar Sokoto, ya ce rufe boda ko iyakar da aka yi bai yi musu dadi ba.
Su kuwa kungiyoyin kare hakkin dan Adam tuna wa Najeriya su ka yi da yarjejeniyar Ecowas ta kai da kawowa a Abuja ta ke, su na cewa ba su jin dadin wannan lamarin na rufe boda ko iyaka kamar yadda Alhaji Abdullahi kado na kungiyar ‘yanci da Walwala ya bayyana.
Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka daga Birni N'Konni, Harouna Mamane Bako.
Facebook Forum