Fiye da makonni hudu bayan da hukumomin tsaro a Najeriya suka gano wasu wuraren Azabtar da bil’adama da sunan cibiyoyin gyara halayen kangararru a garuruwan Kaduna da Daura, masu ruwa da tsaki a na ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan hanyoyin da za a bi domin kawo gyra wajen tafiyar da wadannan cibiyoyi.
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ce dai ta fara bankado cibiya ta farko a jahar Kaduna, inda aka gano yadda magabatan cibiyar ke muzgunawa wadanda aka killace a cibiyar da sunan gyaran hali.
Daga bisani jami’an tsaro suka sake gano makamanciyarta a garin Daura da jahar Gombe.
Samamen da jami’an tsaro su ka rinka kai wa ma irin wadannan cibiyoyi ko makarantu ya sanya masu kula da takwarorinsu a sauran sassa, suka sha jinin jikinsu, tare da daukar matakan tsira da mutunci.
A jihar Kano kididdiga ta nuna akwai makarantun gyran halayen kangararrun mutane kimanin guda 30, wadanda aka fi sani da gidajen Mari.
Malam Ibrahim Liman Sharifai, shugaban makarantar koyon Alqur’ani da gyaran hali ta Limamin Sharifai a cikin birnin Kano, ya ce yawanci tarbiyya ake koyawa mutane, amma da suka fahimci marin da ake sanyawa mutane yana da tasa matsalar sai suka daina sawa.
To amma Malam Ibrahim Liman wanda ya ce makarantarsa na da rijista da hukumomin gwamnatin Kano, ya fayyace dalilan amfani da mari ga kangararrun dalibai.
Sai dai Malam Auwalu Bala Durumin Iya, masanin harkokin laifuka da bincike kan halayyar dan Adam na cewa, akwai bukatar gwamnati ta shigo ciki, don a sanya ka’idoji a irin wandannan cibiyoyi.
Koda yake gwamnatin tarayya ta bada umarnin rufe irin wadannan makarantun a fadin kasar, Malam Abdullahi Idris, shugaban cibiyar magunguna ta Danfodio a Kano ya ce, ya kamata gwamnati kada ta rufe makarantun, amma ta shigo a gyara tsare-tsaren yadda za a tafiyar da su wadannan cibiyoyin.
Ga cikakken rohoton wakilin Muryar Amurka a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari.
Facebook Forum