Cikin manyan matsaloli ko kabulen da za a tattauna a kai a taron na Yini ‘daya a Brussels, shine ko za a ci gaba da kakaba wa kasar Rasha takunkumi game da batun Ukraine da matsalar bakin haure a Turai da kuma shawarar da Birtaniya ta yanke na fita daga kungiyar tarayyar Turan.
An shirya cewa Fara Ministar Birtaniya Theresa May, za ta bar taron da wuri kafin sauran shugabannin 27, wadanda daga baya zasu hadu don cin abinci su kuma tattauna kan fitar Birtaniya daga kungiyar.
Rashin gayyatar Theresa May zuwa liyafar da aka shirya, shine alamar farko da ta fito fili dake nunawa a zahiri cewa Birtaniya, wadda ke zama kasa ta biyu a tattalin arziki a Nahiyar Turai, za ta raba gari da kungiyar. A wata sanarwa, mai magana da yawun May, ya so ya nuna kamar ba wani komai, game da wannan al’amarin da wasu ke fassarawa da gwale Shugabar ta Burtaniya.
Akan Rasha kuwa, babu wani abin bazata da ake tsammani. A farkon makon nan ne shugabar Jamus Angela Markel da shugaban kasar Faransa Francois Hollande, su ka ce zasu goyi bayan tsawaita takunkumin da aka kakaba wa Rasha saboda batun Ukraine. An yanke wannan shawarar ce duk kuwa da karin matsin lamba daga masu zuba hannun jari a fannin makamashi a Turai, ciki har da ita kanta Jamus kan cewa a ci gaba da takunkumin.