Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Nada Shugaban Kamfanin ExxonMobil Sakataren Harkokin Waje


Donald Trump da Rex Tillerson mutumin da ya nada sakataren harkokin waje
Donald Trump da Rex Tillerson mutumin da ya nada sakataren harkokin waje

Shugaban Amurka mai jiran gado, Donald Trump,ya bada sanarwar nada shugaban kampanin man fetir na ExxonMobil mai suna Rex Tillerson a matsayin sabon skakataren harkokin wajen Amurka.

Tillerson wanda ya kasance aboki na shugaban Rasha ya kwashe kimanin shekaru 41 yana aiki a wannan kampanin man fetir din na ExxonMobil.

Trump yace Tillerson masani ne a harkan gudanar da wannan kampanin dake daya daga cikin manyan kampunnan man fetur na duniya,kuma wannan nadin ya ta'allaka ne akan kwarewarsa da zai taimakeshi gudanar da ma’aikatar harkoki wajen Amurka.

Sai dai ana sa ran cewa huldar Tillerson da shugaban Rasha Vladmir Putin zata iya zama wani abin damuwa, a cewar Sanata John McCain, shugaban kwamitin soja a Majalisar Dattawa, wanda ya yi magana a ranar Lahadi kan wannan lamarin.

Shima wani dan majalisar ta dattawa kuma dan jam’iyyar Republican, Marco Rubio yace koda yake Rex Tillerson dan kasuwa ne mai daraja, amma duk da haka yana da damuwa a kan wannan mukami da aka bashi.

XS
SM
MD
LG