Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Donald Trump Zai Bayyana Sunan Wanda Zai Nada Sakataren Harkokin Waje


Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado
Donald Trump shugaban Amurka mai jiran gado

Sabon shugaban Amurka dake jiran gado, Donald Trump yace a yau Talata zai fadi sunan mutumin da zai nada Sakatarensa na Harakokin Waje.

Koda yake Trump bai fayyace ko waye zai baiwa wannan mukamin ba, ana karfafa kyautata zaton cewa watakila shugaban kampanin man fetur na ExxonMobil, Rex Tillerson ne zai baiwa aikin.

Shi dai Tillerson sannanen dan kasuwa ne da ya jima yana kulla dangatakar harakokin kasuwanci da Rasha kuma ance yana ma da dangatakar kut da kut da shi kansa shugaban rasha din, Vladimir Putin – abinda ake ganin zai iya janyo Tillerson matsala idan anzo zaman muhawarar tabattarda shi akan mukamin a gaban ‘yan Majalisar Dattawa.

Yanzu hakan ma ‘yan majalisar na dokokin Amurka suna gudanarda binciken gano ko Rasha ta taka wata rawa wajen yin tasiri a cikin zaben da aka yi a Amurka din a watan jiya, musamman don a gani ko tayi wani abu da ya taimakawa shi Donald Trump lashe zaben.

Kuma daga cikin masu goyon bayan a gudanarda wannan binciken harda giggan ‘yan jam’iyyar Republican ta shi Trump din, kamar shugaban Majalisar Dattawa Mitch McConnell da kuma Kakakin Majalisar Wakilai, Paul Ryan.

XS
SM
MD
LG